Tuesday, June 9, 2020

Koriya Ta Arewa ta katse hanyoyin sadarwa tsakanin ta da Koriya Ta Kudu

Koriya Ta Arewa ta katse hanyoyin sadarwa tsakanin ta da Koriya Ta Kudu

North Korean students take part in a rally denouncing "defectors from the North" as they march from the Pyongyang Youth Park Open-Air Theatre to Kim Il Sung Square in Pyongyang on June 8, 2020
Hakkin mallakar hotoAFP
Image captionDalibai a Koriya Ta Arewa sun yi maci don nuna adawa da masu yi wa kasar zagon kasa

Koriya Ta Arewa ta ce za ta katse duk layukan sadarwa na hukuma da Koriya Ta Kudu ciki har da wani layin kiran gaggawa tsakanin shugabannin ƙasashen biyu.

Mahukuntan birnin Pyongyang sun ce wannan ne na farko a jerin matakan da za su ɗauka kan gwamnatin birnin Seoul da suka bayyana da "abokiyar gaba".

Umarnin ya zo ne daga Kim Yo-Jong 'yar uwar Shugaba Kim Jong Un.

Matakin ga alama wani martani ne ga wasu takardun nuna adawa da gwamnati, da 'yan Koriya Ta Arewa da suka sauya sheƙa bayan sun tsere zuwa kudanci suka riƙa jefawa ƙasar ta sama.

Mai aiko da rahotanni daga birnin Seoul na cewa sanarwa na iya zama wata dabarar tayar da rikici daga Koriya Ta Arewa da fatan amfani da ita a matsayin madogara a tattaunawar da za su iya yi nan gaba.

A bayyane yake cewa har yanzu Arewa da Kudu na yaki da juna saboda babu wata yarjejniya da aka cimma a lokacin da yakin Kotiya ya kawo karshe a shekarar 1953.

Koriya Ta Arewa za ta katse dukkan alakar da ke tsakanin hukumomin Arewa da Kudu, wanda ake ta amfani da shi ta wani ofishin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu... daga karfe 12 na tsakar daren 9 ga watan Yuni,'' kamar yadda kamfanin dillancin labaran Arewa KCNA, ya fada.

Sannan za a katse hanyoyin sadarwar soji, in ji Koriya Ta Arewar.

A lokacin da aka rufe ofishin da ke sada alaka tsakanin kasashen biyu a watan Janairu saboda annobar Covid-19, kasashen biyu sun ci gaba da alaka ne ta wayar tarho.

Kasashen biyu su kan yi waya sau biyu a rana da karfe 9 na safe da kuma 5 na yamma. A ranar Litinin ne Kudu ta ce ba a dauki wayar da ta buga da safiya ba a karon farko cikin wata 21, duk da cewa dai sun ji daga juna da rana.

KCNA ya ce: "Mun yanke shawarar cewa babu bukatar zama gaba da gaba da hukumomin Koriya Ta Kudu kuma babu wani abu da za mu tattauna da su, don ba abin da hakan ke karawa sai sanya mana zato da shakku.''

A makon da ya gabata ne 'yar uwar shugaban Koriya Ta Arewa Kim Yo-jong ta yi barazanar rufe ofishin huldar har sai Kudu ta dakatar da kungiyoyi masu adawa da gwamnati na 'yan Koriya Ta Arewa da suka sauya sheƙa suka tsere Kudu daga aika sako da suke yi Arewar.

Ta ce takardun fafutukar da suke aikewa din sun kauce wa yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekarar 2018 tsakanin shugabannin kasashen biyu.

Previous Post
Next Post

0 Comments: