Thursday, August 13, 2020

Tsiyayar man Mauritius: Me ya sa tasirinsa zai iya yin muni sosai ga Muhalli?

 

Tsiyayar man Mauritius: Me ya sa tasirinsa zai iya yin muni sosai ga Muhalli?

  • Daga Navin Singh Khadka
  • Wakili kan muhalli
ASALIN HOTON,GREENPEACE

Bayanan hoto,

Jirgin ruwan Japan, MV Wakashio, ya ratsa kusa da tsibiri a tekun Indiya a karshen watan Yuli. kuma ya fara tsiyayar da mai a Alhamis din da ta gabata

Ruwan serene turquoise da ake kira Blue Lagoon a wajen ƙauyen Mahebourg a Mouritius, inda yawanci ake fina-finan Indiya yanzu ya gurɓace ya koma baƙi.

Jirgin ruwan Japan, MV Wakashio, ya ratsa kusa da tsibiri a tekun Indiya a karshen watan Yuli, kuma ya fara tsiyayar da mai a Alhamis din da ta gabata.

Wasu hotuna daga Intanet ya nuna yadda tsiyayar man ke faɗaɗa daga tsakiyar Mouritian a Pointe D'Esny zuwa tsibirin Ile-aux-Aigrettes.

Ana tunanin kusan tan 1,000 na mai ya tsiyaye daga jirgin zuwa cikin ruwan, wanda ya haifar da aikin tsabtace ruwan.

Amma ba wai yawan tsiyayar ba ne ke da matukar tayar da hankali ba - wurin da tsiyayar ke faruwa ne ke haifar da babbar barazanar mummunar illa ga muhalli.

ASALIN HOTON,AFP

Bayanan hoto,

Masu agaji na son rage yawan tsiyayar man

Ko da yake yawan man da ya tsiyaya kaɗan ne idan aka kwatanta da da manyan tsiyayar man da aka gani a duniya a baya amma kuma ɓarnar da hakan zai haifar babba ce, kamar yadda masana suka ce.

Ba kamar tsiyayar man da aka samu ba a baya, wannan ya faru ne a wurin ruwan da aka kare kuma aka tabtace da wurin shaƙatawa na Blue Bay, wanda ke da da muhimmanci sosai a duniya.

Wuri mai nau'in halittu

Mauritius wuri ne mai halittu musamman tsirrai da dabbobi a yankin.

ASALIN HOTON,SUNIL MOKSHANAND

Bayanan hoto,

Tsiyayar ta riga ta bazu a yankunan gabar teku

Iska da ruwa ba su taimakawa, domin suna malalar da man zuwa yankin da ke da muhimmanci, kamar yadda Sunil Mokshanand, masananin muhalli ya shaida wa BBC daga yankin kusa da inda man ke malala.

Ruwan Mouritania na da halittu 1,700 da suka kunshi nau'in kifaye 800, da nau'in kunkuru guda biyu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

ASALIN HOTON,GREENPEACE

Bayanan hoto,

Ana tunanin jirgin MV Wakashio na ɗauke da ton 4,000 na mai, inda kusan kwatar man ya tsiyaye a ruwan

Irin wannan ruwan masu arzikin halittu ba su da yawa a duniya. Kuma malalar mai irin wannan zai yi tasiri sosai ga dukkanin abin da ke ruwan," a cewar Dakta Corina Ciocan, babbar malama a ɓangaren ilimin halittun ruwa a jami'ar Brighton.

Ana tunanin jirgin MV Wakashio na ɗauke da ton 4,000 na mai, inda kusan kwatar man ya tsiyaye a ruwan.

Duk da rashin kyawon yanayi mai kyau, Firaministan Mauritania Praving Jugnauth a ranar Laraba ya ce an cire dukkanin man da ke cikin tankar jirgin, ko da yake akwai sauran man a ciki.

Ana fargaba kan jirgin ruwan zai iya karyewa, kuma man zai ƙara haifar da tsiyayar man.

An sauya man zuwa wani jirgin ruwan wani kamfanin Japan ta hanyar helikwafta.

ASALIN HOTON,SUNIL MOKSHANAND

Bayanan hoto,

Tsiyayar ta shafi tsirrai da dama

Har yanzu ba a tantance yadda jirgin ya ratso ta wurin shakatawar ba a ruwan amma ƴan sanda na gudanar da bincike.

A wani taron manema labarai, Akihiko Ono mataimakin shugaban Mitsui OSK Lines, ya nemi afuwar tsiyayar man da kuma abin da ya kira "girman barnar da suka hakan ya haifar."

ASALIN HOTON,GREENPEACE

Bayanan hoto,

Masana sun ce tsiyayar barazana ce ga tsirrai

Tasirin tsiyayar mai

Tsiyayar mai aka gani a sassan duniya ya yi shafi dabbobi da tsirrai.

A 2010, tsiyayar da ta faru a ruwan Mexico kusan ton 400,000 na mai ya tsiyaye, wanda ya haifar da mutuwar dubban halittu.

Akwai kuma wasu tasirin kan halittu a ruwa da suka hada da haihuwa da kuma cuttuka.

ASALIN HOTON,GREENPEACE

Bayanan hoto,

Ana fargaba kan sauran man da ke cikin jirgin zai ci gaba da tsiyaya

A 1978, wata babbar tankar mai - Amoco Cadiz - ta ratsa ruwan Birtaniya da Faransa, inda kusan tan 220,000 na mai ya tsiyaye.

Kusan kilomita 320 na ruwan Faransa tsiyayar man ya gurɓata, kuma ya kashe miliyoyin halittu.

Tsiyayar ta kuma kashe kusan tsuntsaye 20,000 tare da gurɓata tsirrai a yankin.

Masana sun ce duk da ƙokarin da ake amma yawanci kashi 10 kawai na tsiyayar mai ake tsabtacewa.

Farfesa Richard Steiner. ya ce dole gwamnatin Mauritania dole ta yi bincike cikin hanzari. Ya ce " Yadda aka yi saurin ɗauke sauran man labari ne mai kyau amma abin da ya riga ya tsiyaye abu ne mai jan hakali kuma da zai yi barna.

"Akwai yiyuwar tasirin zai ɗauki shekaru."

Previous Post
Next Post

0 Comments: