Monday, May 25, 2020

Covic 19: A Nigeria Mutum 229 sun sake kamuwa, 233 sun mutu

         

@NCDCgovHakkin mallakar hoto@NCDCGOV
Image captionTun bayan ɓarkewar annobar korona, Najeriya ta yi ƙoƙarin ƙara yawan cibiyoyin gwaje-gwaje da horas da jami'an lafiya

Sabbin alkaluman da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta fitar a daren Litinin sun nuna cewa wadanda suka kamu da cutar korona sun haura dubu takwas a Najeriya.

Alkaluman da ta fitar da misalin 12 saura sun nuna cewa mutum 229 sun sake kamuwa, hakan ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar 8,068.

Haka kuma hukumar ta ce wadanda suka mutu sun kai 233 a fadin kasar.

Har yanzu dai Jihar Legas ke kan gaba an samu karin mutum 90 da suka harbu, sai Katsina da ke mataki na biyu da mutum 27.

Jihar Imo na da mutum 26 sabbin kamu, sai Kano da alkaluma suka nuna an sake samun mutum 23 dauke da cutar.

Birnin Tarayya Abuja na da mutum 14, Plateau 12, Ogun 9, sai Delta 7.

Karin bayani kan coronavirus

Sauran jihohin da suka fito a jadawalin sun hada da Borno mai mutum 5, Rivers ita ma mutum 5, Oyo kuma mutum 4.

Masu cutar korona a Gombe sun karu da 3, Osun 2, kana akwai Anambra da Bayelsa inda aka samu mutum dai-daya.

Sai dai, daidai lokacin da ake ƙara samun adadin mutanen da cutar ke ƙara harba, haka kuma mutanen da suke warkewa su ma suna ƙaruwa. Yanzu dai mutum 2,311 ne aka tabbatar sun warke a Najeriya.

Kusan rabin mutanen da suka sake kamuwa da koronan suna Lagos, jihar da ta fi fama da annobar a Najeriya. Yanzu dai tana da masu cutar 3,595.

Jihar Kano ita ce ta biyu da yawan masu korona 919, sai Abuja na Uku da yawan masu korona 519.

Har yanzu a hukumance cutar korona ba ta ɓulla cikin jihohin Kogi da Cross river ba, amma wasu na cewa mai yiwuwa akwai annobar cikinsu, kawai dai don ba a yin gwaji ne.

Muhimman bayanai kan annobar korona

An fara gano cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an sallame su daga asibiti.

A ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin korona a kasar.

Gwamnoni irinsu Bala Mohammed da Nasir El-rufa'i da kuma Seyi Makinde na jihar Oyo duk sun kamu da annobar kafin su warke daga bisani.

Har yanzu a hukumance ba a samu bullar cutar a jihohin Kogi da Cross river ba, amma wasu na da ra'ayin cewa hakan ta faru ne saboda ba a gwajin cutar a cikin johohin biyu.

Hukumomin Najeriya dai sun ce sun rubanya adadin gwaje-gwajen da suke yi a kasar, inda a yanzu suka ce akan yi gwaji kimanin dubu guda cikin sa'a 24.

Ga jerin bayanan jihohin da korona ta bulla cikinsu ya zuwa daren Litinin 25 ga watan Mayu.

NCDCHakkin mallakar hotoNCDC


Shafinmu na Facebook
Ko kuma ta email address
madubiya@gmail.com
Previous Post
Next Post

0 Comments: