Ibrahim Gambari: Wane ne sabon Shugaban Ma'aikatan fadar Shugaba Buhari?

Shugaban Najeriya, Muhammad Buhari ya amince da nadin Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadarsa.
Farfesa Ibrahim Gambari wanda gogaggen masani diplomasiyya ne ya maye gurbin marigayi Mallam Abba Kyari wanda ya rasu kimanin wata guda sakamakon kamuwa da cutar korona.
Kafin dai nada Farfesa Gambari, sunayen da suka yi ta kai-komo a jaridu da bakunan 'yan Najeriya da ake alakantawa da mukamin su ne Babagana Kingibe da Adamu Adamu da Hameed Ali da ma gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai.

Wane ne Farfesa Ibrahim Gambari?
Farfesa Ibrahim Gambari fitaccen malamin jami'a ne kuma ma'iakacin diflomasiyya da ya rike mukamai manya-manya a duniya da Afirka da kuma Najeriya.
- An haifi Ibrahim Gambari a shekarar 1944, a Ilorin, jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.
- Gambari ya yi sakandarensa a King's College da ke Lagos. Ya yi digirinsa na farko a London School of Economics inda ya kammala a 1968 kuma ya samu kwarewa a fannin harkokin kasashen waje.
- Ya yi digirinsa na biyu da na uku a 1970 da 1974 a jami'ar Columbia University, New York d ake Amurka a fannin kimiyyar siyasa da harkokin kasashen waje.
- Daga nan sai Farfesa Gambari ya koma jami'ar Ahmadu Bello University da ke Zaria a jihar Kaduna inda ya koyar daga 1977 zuwa 1980.
- Farfesa Ibrahim Gambari ya kasance mutum na farko da ya zama Magatakardar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya kuma bai ba da shawara na musamman ga Sakatare Janar na Tarayyar Afirka,
- A shekarar 1984 zuwa 1985 Ibrahim Gambari ya zamo ministan harkokin wajen Najeriya.
- Ibrahim Gambari ya sake zama ambasada kuma wakilin Najeriya na dundundun a Majalisar Dinkin Duniya a 1990 zuwa 1999.
- A 1999 din dai Gambari ya kasance Shugaban Kwamitin gudanarwa na UNICEF.
- A 2012 Gambari ya jagoranci kwmaitin wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka a Darfur daga 2010 zuwa 2012.
- Gambari ya lashe karramar Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ga wadanda ba 'yan kasa ba a 2012.
- Farfesa Ibrahim ya zamo shugaban jami'ar jihar Kwara na farko a 2013.
- Ibrahim Gambari ne mutumin da ya kafa cibiyar bincike ta Savannah Centre for Abuja.

0 Comments: