COVID-19: Gwamnati ta cin ma matsaya da ‘Yan Majalisa kan zaftare 30% a albashinsu
Jaridar The Tribune ta bayyana cewa ‘yan majalisar Oyo sun cin ma matsaya da gwamnatin Seyi Makinde game da kason da za a rage daga cikin kudin da su ke karba a kowane wata.
Rahotannin sun ce ‘yan majalisar dokokin za su hakura da kashi 30% na kudinsu.
Wannan ragi zai fara tasiri ne daga albashin watan Afrilu har sai zuwa lokacin da abubuwa su ka mike.
Mai magana a madadin majalisar dokokin jihar Oyo, Honarabul Kazeem Olayanju, ya shaida cewa shi da abokan aikinsa sun yi wannan ne domin a iya gudanar da sha’anin gwamnati.
Ya ce: “An rage 30% daga cikin abin da mu ke samu a matsayin gudumuwarmu na yaki da annobar COVID-19. Gwamnan ya kawo wannan shawara, kuma mu ka amince da hakan.”
Gwamna Seyi Makinde ya nunawa ‘yan majalisar jihar cewa gwamnatin tarayya ta rage abin da ta ke ba jihar Oyo da kashi 60% a sakamakon annobar Coronavirus da ake fama da ita.
Bayan haka, gwamna Makinde ya yi irin wannan kira ga sauran masu rike da kujeru da manyan mukaman siyasa da su sadaukar da wani abu daga cikin makudan kudin da su ke samu.
Kazeem Olayanju ya ce hakan zai taimaka wajen ganin gwamnatin Oyo ba ta kai ga rage albashin da ake biyan ma’aikata a daidai lokacin da wannan annoba ta zaunar da jama’a a gida.
Wannan annoba da ake fuskanta ta yi sanadiyyar karya farashin gangar danyen mai a Duniya. A dalilin haka Najeriya wanda ta dogara da mai ta yi wa kasafin kudin 2020 garambawul.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a:
madubiya@gmail.com
0 Comments: