Tuesday, April 7, 2020

Yadda jami'an Tsaro suka gano gidan da ake 'TSAFI' a zamfara.



Hakkin mallakar hRUNDUNAR 'YAN SANDAN JIHAR ZAMFARA TA CE TA TARWATSA WANI GIDAN DA AKE ZARGIN NA MATSAFA NE A GARIN GUSAU INDA TA SAMU WASU TAKARDU DAUKE DA SUNAYEN MANYAN 'YAN SIYASA A JIHAR.


Kwamishinan 'yan sandan jihar Usman Nagogo, a wani taron manema labarai ya ce jami'ansa sun kai samame ne gidan matsafan da ke Unguwar Dallatu bayan samun rahoto daga mutanen anguwar a ranar Litinin.

Ya ce sun samu abubuwa da dama da suka hada da: "Kwaryar jini da kwarya an sossoke allurai da wata tukunya dauke da gari da kuma takardun da aka rubuta sunayen shahararrun mutane a Zamfara."

"Ba zan iya tabbatar da sunaye ba, amma manyan sunayen 'yan siyasa ne a jihar," in ji Kwamishinan 'yan sandan.

Ya kara da cewa zai aika da jinin da aka samu a kwarya a asibiti domin tabbatar da ko jinin mutum ne ko na dabba.

A nata bangaren gwamnatin Zamfara ta ce tuni ta bayar da umurni aka rusa gidan, kamar yadda Zailani Baffa mai magana da yawun gwamnan jihar ya shaida wa BBC.

Ya kuma ce 'Yan sanda ne za su gudanar da bincike kan lamarin, "bincike ba hakkin gwamnati ba ne," inji shi.

Babu dai wanda 'yan sandan suka kama a gidan da ake zargin ana tsafin, inda kwamishinan 'yan sandan jihar ya ce mutum biyu da aka iske a gidan dukkaninsu sun tsere.

Amma ya ce tuni rundunar 'yan sandan ta kaddamar da bincike kan al'amarin, kuma za a sanar da al'umma abin da binciken ya gano.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce an sha samun irin wannan matsala ta masu mugunyar fata, masu daukar Al Kur'ani mai tsarki su jefa a masai ko su kone makabarta a Jihar Zamfara da ke fama da matsalar 'yan bindiga masu fashin daji da satar mutane.

Previous Post
First

0 Comments: