Wednesday, May 13, 2020

Coronavirus; Da gaske shinkafan da Nigeria take rabawa mara kyauce

Coronavirus; Da gaske shinkafan da Nigeria take rabawa mara kyauce

Jollof riceHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Dubban buhunhunan shinkafar da gwamnatin tarayyar Najeriya take rabawa a matsayin tallafi na kullen annobar cutar korona ya matukar harzuƙa mutane.

Wasu jihohin sun yi ƙorafin cewa shinkafar da aka rarraba musu ɗin wadda ta lalace ce kuma ba za a iya cin ta ba.

A watan da ya gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa jami'an fasa ƙwabrin ƙasar umarnin raba buhunhunan shinkafar da aka kwace, ga mabuƙata don taimaka musu wajen halin da za su shiga a lokacin kullen da aka sanya don hana yaɗuwar cutar korona.

Amma tallafin bai yi wa wasu dadi ba a wasu jihohin a kudu maso yammacin ƙasar, waɗanda su ne suka fara karɓar taimakon.

Jihar Oyo da jam'iyyar adawa ta PDP ke mulkinta ta fi kowa yin ce-ce-ku-ce kan rashin kyawun shinkafar, ta kuma rubuta wasiƙa ga hukumar fasa ƙwabri (Kwastam), kan niyyarta na mayar wa hukumar lalatacciyar shinkafar mai ƙwari.

A ranar Laraba kuwa jihar ta yi aiki da wannan barazanar inda ta mayar da buhun shinkafa 1,800 cikin manyan motoci biyu, inda aka ajiye su ba tare da kulawa ba a gaban hukumar, bayan da jami'an kwastam ɗin suka ki karba.

A jihar Ondo kuwa, inda jam'iyyar APC ke mulki, jami'ai sun ce wasu buhunhunan na dauke da shinkafar da ta lalace kuma ba zai yiwu a ci ta ba, amma dai ba su dauki matakin mayar da ita ba.

Amma hukumar kwastam ta Najeriya ta karyata batun cewa shinkafar da ta bayar marar kyau ce, ta kuma ce jihar Oyo ta ba ta kunya kan waɗannan zarge-zarge da ta yi.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce, ''Babu wata alama ta shinkafa marar kyau a rumbun adana kayayyakinta, sannan kuma babu alama ma bayan an loda ta a manyan motoci.''

A man carrying bags of riceHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMafi yawan 'yan Najeriya sun sayi abinci da yawa sun jibge a gida bayan da gwamnati ta sanar da daukar matakin kulle a wasu jihohin kasar

Ministar Ma'aikatar Jin ƙai Sadiya Farouq, wadda ma'aikatar tata ce ke aikin raba shinkafar ta kara jawo ce-ce ku ce.

Ta ce sai da Hukumar Kula Da Ingancin Abinci Da Magunguna Ta Najeriya, NAFDAC ta duba shinkafar sosai ta kuma amince da ita.

Amma shugabar Nafdac, Mojisola Adeyeye, ta ce ba a gayyaci hukumar ta duba shinkafar da aka raba a Oyo kamar yadda ministar ta yi ikirari ba.

Daga ina shinkafar ta fito?

Akwai dubban buhunhunan shinkafa da suka shafe watanni a rumbun ajiya na hukumar kwastam tun bayan da aka ƙwace su daga masu fasa ƙwabrin da suke ƙoƙarin shiga Najeriya.

Kuma daga cikin wannan shinkafa ce hukumar ta bayar da tan 46,000 don a raba wa jihohi sakamakon umarnin da shugaban ƙasa ya bayar.

A watan Agustan bara ne aka rufe kan iyakokin Najeriya don hana shigar da kayayyakin da suka hada da shinkafa cikin ƙasar.

Kuma ga alama ba al'ummar kudu maso yamma ne kadai suka yi korafi kan shinkafar ba.

Wani mai amfani da shafin Tuwita ya wallafa wani bidiyo na buhun shinkafar ''Tallafin Covid-19'' wato "Covid-19 Palliative" da hukumomin birnin tarayya Abuja suka bai wa mazauna wani yanki, inda ya bayyana shinkafar da cewa ''mai guba ce kuma ta lalace.''

Presentational white space

Wannan ne karo na farko da irin haka ya faru?

An taba samu a tarihi inda jami'an gwamnati suka tabbatar da cewa wasu buhunhunan shinkafa da kwastam suka kwace sun lalace kuma ba za a iya cin shinkafar ba.

A watan Oktoban bara, Shugaban Hukumar Kwastam Ta Najeriya, Hameed Ali, ya ce shinkafar waje da ake fasa ƙwabrinta 'yan ƙasar suke ci mara kyau ce wacce ta lalace, shi ne ake sake mata buhu a shigar da ita ƙasar ta ɓarauniyar hanya.

Ya ce: ''Haka suke yi a Jamhuriyyar Benin. Suna sauya buhun su saka sabon kwanan wata, kuma ita ake kawowa muna ci a ƙasar nan.''

Wata hadimar shugaban ƙasa Lauretta Onochie ta wallafa wannan bidiyon na kasa da ke nuna dubban buhunhunan shinkafa da aka ƙwace waɗ anda ta ce sun lalace.

''Ba mu san yaushe aka girbe ta ba. Ba mu san irin sinadaran da aka sanya wajen adana ta ba,'' kamar yadda ta fada a tuwita.

Presentational white space

Dafaffiyar shinkafa, musamman ma dafa-duka, na daga cikin irin abincin da ke da farin jini a kasar, kuma ɗanyar shinkafar ce muhimmiyar abar da kungiyoyi da mutane suke raba wa marasa galihu a lokacin wannan kullen.

Previous Post
Next Post

0 Comments: