Saturday, May 16, 2020

COVID-19: YA DACE MU JIJJINA GA MATAKAN DA GWAMNA TAMBUWAL YA DAUKA GA AL'UMMARMU TA SOKOTO.

COVID-19: YA DACE MU JIJJINA GA MATAKAN DA GWAMNA TAMBUWAL YA DAUKA GA AL'UMMARMU TA SOKOTO.




Kuji tsoron mutum shiru shiru inda duk yake, mussaman mai hakuri, don kuwa randa duk ya furta zai yi, babu shakka ba fashi sai ya aikata.

Mutanen jihar Sokoto ba karamar sa'a ne Allah Yayi mana ga samun shugabanci irin na Rt. Hon Aminu Waziri Tambuwal, CFR (Mutawallen Sokoto) a cikin wannan yanayi irin yanzu ba; don kuwa mun ga misalai da yawa, tun ma ba daga irin matakan da ya dauka da neman sassaucin wanda ya nuna akan abin da ya shafi tsaurarawa da akaso ayi mana dangane da bullar cutar Coronavirus ko COVID-19 a jaharmu ba. 
Komi kiyyayarka ko rashin kaunarsa, ya san akwai sauki akan yadda ya zauna da masu ruwa da tsaki, Sarakuna, Malamai da sauran jama'a don fitowa jahar nan da makomar da ta dace da ita, ga yaki da wannan cutar.

Hakika wadanan matakian da hangen nesan da  Gwamna Tambuwal yayi ya sanya yanzu ga Borno da Gombe na kwaikwayonsu ga komawa akan hanyar yin sassauci da bayar da izni na gudanar da sallalolin farilla, cin kasuwa da walwala ga jama'arsu kamin matakin gwamnatin tarayya na 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe ya kammala aiki.
Idan da Mai girma gwamna bai yi.hangen nesan daukar matakin da ya dauka ba, watakila da sassaucin.da ake gani bai kai na yanzu ba.

Yanzu a Jahar Sokoto ba a rufe Massalatai na Jumu'a da Salloli biyar, ba a hana cin kasuwa ko mu'amala tsakaninku da rana ba; an baiwa kowa dama yayi kasuwanci tare da hulda bisa kulawa da bin dokoki da shawarwari.

Hakan ya sanya jama'a samun dama na yin addu'oi da rokon Allah akan wannan masiifar da sauran wasu a cikin al'umma abin da muke fata nan gaba kadan za a janye sauran dokokin.

Don haka mu dage a cikin wannan karshen kwanakin nan gima da suka rage muyi ibada da rokon Allah (SWT)/ga samar muna sauki a jaharmu da kasarmu da duniya baki daya.

Mu yiwa shugabanmu, Gwamna Tambuwal da sauran wadanda aka dora ma aikin nan addu'a da fatan samun nasara akan wannan hanyar da aka dauko na saukake wahalhalun dake tattare da wannan cutar da irin yawan hare-haren ta'addanci a wasu garuruwa na gabashin jaharmu.

Yiwa Mai girma Gwamna Tambuwal addu'a akan wannan yanayin, tabbata tamkar yiwa kai ne da jahar baki daya ga kowane dan haifen jahar nan.

Samun nasara da taimakon Allah garesa na ya tsaya tsam ya ci gaba da abin da ya fara, hakika amfaninmu ne gaba daya a jiharmu.

Babu siyasa ko zama dan cikin gida akan wannan lamarin. Mu duka yan jaharnan ne, duk wata barazana ko cika baki ko tayar da jijjiyoyin wuya ga kowane mutum, basu da amfani ga wannan halin da ya wuce addu'a da fatan nasara.

Muhimman batu shine mu samu nasarar ficewa daga wannan jarrabawa mai dauke da wahala da barazana ga
 makomarmu baki daya anan gaba.
Hakika ita dai COVID-19 za a ci gaba da zama da ita a cikin al'umma har lokacin da Allah Ya kawo karshenta, hakan zai zama abin bukata garemu na kiyaye dokokin yaki da ita a cikin mu.

Duk wata dubara ko sanin hanya bai kai kaucewa daga zama cikin dalilan kara yaduwarta da ake faman yi ba.
Muna fatan samun sassauci daga Shugaban kasa na dokar nan ta dare don kara baiwa jama'a dama suyi azama ga ibada da bunkasa sana'oinsu baki daya.
Wasu masu fataucin dare na bukatar agajin Gwamnatin tarayya don takaita dokar dare da rage karfinta ga samun sauki na walwala a wurarensu.

Allah Ya taimaki jaharmu baki daya.
Amin.

Daga
- Yusuf Dingyadi, Sakkwato

Zaku iya tuntuban mu a kafa namu na Facebook
www.facebook.com/jmadubiya
To ta address namu
madubiya@gmail.com
Previous Post
Next Post

0 Comments: