Thursday, June 25, 2020

APC~ NWC ta kalubalanci Shugaba Buhari, Akoi yiyuwar a shigar da kara a gaban kotu

Main Labarai LABARAISIYASA APC - NWC ta kalubalanci Shugaba Buhari, akwai yiwuwar a shigar da kara a gaban kotu 11 minutes ago 74 views by  Muhammad Malumfashi A ranar Alhamis ne jam’iyyar APC ta kir taron majalisar koli ta NEC, inda aka sauke daukacin majalisar NWC mai alhakin gudanar da harkokin jam’iyya, wannan mataki ya bar baya da kura. Wasu daga cikin ‘yan majalisar NWC ta jam’iyyar APC da aka ruguza a wajen taron NEC sun ce su na tuntubar Lauyoyi da masu ruwa da tsaki domin yanke shawara game da matakin da za su dauka. Majalisar NEC ta zabi Alhaji Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe kuma tsohon sakataren jam’iyyar APC na kasa a matsayin shugaban rikon kwarya wanda zai gudanar da sabon zabe. 



Main Labarai LABARAISIYASA APC - NWC ta kalubalanci Shugaba Buhari, akwai yiwuwar a shigar da kara a gaban kotu 11 minutes ago 74 views by  Muhammad Malumfashi A ranar Alhamis ne jam’iyyar APC ta kir taron majalisar koli ta NEC, inda aka sauke daukacin majalisar NWC mai alhakin gudanar da harkokin jam’iyya, wannan mataki ya bar baya da kura. 

Wasu daga cikin ‘yan majalisar NWC ta jam’iyyar APC da aka ruguza a wajen taron NEC sun ce su na tuntubar Lauyoyi da masu ruwa da tsaki domin yanke shawara game da matakin da za su dauka. Majalisar NEC ta zabi Alhaji Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe kuma tsohon sakataren jam’iyyar APC na kasa a matsayin shugaban rikon kwarya wanda zai gudanar da sabon zabe. 

Tsofaffin shugabannin jam’iyyar ta APC a majalisar Adams Oshiomhole, wanda kotu ta dakatar, sun nuna cewa ba su gamsu da wannan mataki da manyan jam’iyyar su ka dauka a taron NEC ba. Victor Giadom ne ya kira wannan taro, wanda ‘ya ‘yan NWC su ka ki halarta, kuma su ka ce zaman da aka yi ya sabawa doka domin ya ci karo da sashe na 25(B) na tsarin mulkin jam’iyya.
 A doka, shugaban jam’iyya ne kurum zai iya kiran taron NEC, haka zalika sai an bada sanarwar kwanaki 7 zuwa 14 kafin a iya kiran taron lokaci bayan lokaci da kuma zaman gaggawa a APC.


APC NEC Hoto: Twitter Source: UGC 

Duk da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja-kunnen ‘ya ‘yan APC a kan yi wa matakin da aka dauka kunnen-uwar-shegu, tsofaffin ‘Yan NWC sun nuna rashin gamsuwarsu da jam’iyyar. Wadanda ke rike da shugabancin APC a da, sun fitar da jawabi cewa: “Mun lura cewa Victor Giadom ya kira kuma ya jagoranci taron NEC na jam’iyya, inda har aka dauki wasu matakai.”

Jawabin ya kara da cewa: “Yayin da NWC ta ke lura da takaddamar da ke faruwa, za ta tattauna da masu ruwa da tsaki da tarin Lauyoyi a game da matakin da za ta dauka na gaba.” 

Wadanda su ka sa hannu a jawabin sun hada da: Hilliard Eta, Waziri Bulama da Lanre Issa-Onilu. Hilliard Eta ya kasance shugaban APC na shiyyar Kudu maso kudu, inda Waziri Bulama ke rike da ofishin sakataren jam’iyya, sai kuma Lanre Issa-Onilu, wanda ya rike magana da yawun jam’iyya. 

Yayin da NEC ta bukaci a janye duk wasu kara da ke kotu, watakila NWC ta tunanin kai karar jam’iyya koyu a game da taron na jiya. A ranar Alhamis din ne kuma Abiola Ajimobi ya rasu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: madubiya@gmail.com Latsa wannan domin samun sabuwar Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/jmadibiya 

Twitter: https://twitter.com/madubiya


Previous Post
Next Post

0 Comments: