Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci a Najeriya ta buƙaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da ƴan Najeriya sunayen mutanen da suka sace naira biliyan 800 da ya ce gwamnatinsa ta ƙwato.
Ƙungiyar ta ce ta aika wa shugaban wasika ne ta neman bayanai game da sanin waɗanda suka sace ƙuɗaden da kuma abin da gwamnatinsa ta yi da kuɗin da kuma lokacin da aka ƙwato kuɗaɗen.
Ta kuma buƙaci shugaban ya ba hukumomin yaki da cin hanci da rashawa umurnin ƙaddamar da bincike kan zargin da ta yi cewa an raba wa wasu mutane kimanin naira biliyan 51 daga cikin kuɗaden da da gwamnati ta ce ta ƙwato.
Zuwa yanzu babu wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban ƙasa game da buƙatar da ƙungiyar ta ce ta aika wa shugaban ƙasa.
A sanarwar da ta wallafa a shafinta, ƙungiyar ta ce, "shugaban ƙasa ne da kansa a jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya ya bayyana cewa hukumomin da ke yaƙi da cin hanci da rashawa sun kwato sama da naira biliyan 800."
Ƙungiyar ta ce bayanan da ta ke nema za su tabbatar da gaskiya kan inda ƙuɗaɗen suke tare da ba ƴan Najeriya damar fahimtar tasirin ayyukan da aka gudanar da kuɗaɗen.
0 Comments: