#NorthernLivesMatter: Ƴan Nigeria sun dawo daga rakiyar Shugaba Buhari ne?
Kashe-kashen da suka faru a wasu jihohin arewacin Najeriya a cikin makon nan sun yi matukar harzuka mafi yawan mutanen kasar, inda suke ci gaba da yin Allah-wadai da salon mulkin Shugaba Muhammadu Buhari a fannin tsaron kasar.
An kashe fiye da mutum 130 a rana guda a jihohin Borno da Katsina da Adamawa, sakamakon hare-haren 'yan bindiga da na mayakan kungiyar Boko Haram.
Wannan lamari ya matukar dagawa 'yan Najeriya da dama hankali, inda suke jin cewa rayukansu a yanzu daidai suke da na kiyashi, inda ake bin su har gida ana kashewa.
Sai dai Shugaba Muhammadu Buharin ya fitar da sanarwa inda ya yi Allah-wadai da kashe-kashen tare da jajantawa al'ummar da abin ya shafa.
Tuni aka kirkiri wani maudu'i a shafin Twitter mai taken #NorthernLivesMatter, wato Rayuwar 'Yan arewa na da muhimmanci. Kuma har an yi amfani da maudu'in fiye da sau 25,000 zuwa safiyar Alhamis.
Wannan maudu'i ba komai ake tattaunawa akansa ba face irin yadda mutane ke ganin rayukan 'yan arewacin kasar musamman wadanda suke zaune a karkara na cikin barazana a ko yaushe.
Sannan tattaunawar ta mayar da hankali wajen cewa Shugaba Buhari ya gaza da kuma irin "rikon sakainar kashin" da yake yi wa matsalar tsaro a arewacin kasar.
Wasu hotuna da ake ta yadawa na yadda 'yan bindiga ke shiga kauyukan jihar Katsina a kan babura da tsakar rana rike da manyan bindigogi a hannunsu sun kara tayar wa mutane hankali, da tunanin idan har an kai lokacin da masu aikata laifi za su samu kwarin gwiwar hawa titunan Najeriya a bayyane haka don zuwa ta'addanci, to lallai babu wani sauran abin fata a wannan gwamnati.
Mutane da dama sun yi ta yada tsofaffin bidiyo da ke nuna Shugaba Buhari a lokacin da yake yakin neman zaben shugaban kasar inda yake yin tir da Allah-wadai da gwamnatin Goodluck Jonathan ta PDP kan yadda ta gaza a wajen shawo kan matsalar Boko Haram.
Abdul Gidado ya wallafa shafin wasu jaridu da aka wallafa a 2013 inda Shugaba Buhari ya bukaci Jonathan ya sauka daga mulki saboda gazawarsa a harkar tsaro. Sannan sai ya rubuta cewa: "To yanzu kuma sai mu cewa Buhari da Tinubu da Aisha Buhari su sauka kenan kamar yadda suka bukaci wani ya yi a baya"? #NorthernLivesMatter
Shi ma wani @UmarZubyr ya wallafa wani bidiyon Buharin ne a wata hira da aka yi da shi a 2015, inda yake cewa "@MBuhari a shekarar 2015 ka ce babban abin kunya ne ganin yadda tsohuwar gwamnatin Goodluck ta gaza magance matsalar 'yan ta'adda har shekara biyar sannan ya bige da neman taimakon makwabtan kasashe.
''Yanzu ga shi cikin shekara biyar da kai ka yi a kan mulkin, baya ga kungiyar Boko Haram da ke ci gaba da ragargaza, ga kuma matsalar 'yan bindiga wanda sabon abu ne." #NorthernLivesMatter
Ameenu Dauda ko cewa ya yi: ''Zuwa ga @MBuhari, don Allah ka yi murabus idan har ba za a ka iya kare rayukanmu ba... Wannan ne babban dalilin da ya sa aka zabe ka ka hau mulkin nan. #NorthernLivesMatter''
Wasu da dama kuma sun fara zargin kansu a matsayin su na 'yan arewa da cewa su suka zabi Buharin don kasancewar sa daya daga cikinsu kuma wanda suka sa ran zai share musu hawaye, amma sai ga shi wankin hula na neman kai su dare.
@hauwa_farouk ta rubuta cewa: "'Yan arewa sun zabi Buhari ne kawai saboda ya fito daga yankinsu, da kuma kyawawan halayensa, ta haka 'yan siyasar Najeriyar suke yin amfani da bambancin kabila da akidu a matsayin wata dama ta cin zabe, amma tun a shekarar farko ta hawansa mulki wasu masu hangen nesa suka gano cewa ba zai iya mulkin nan ba." #NorthernLivesMatter
Daga cikin dubban ra'ayoyin da BBC ta gani kan wannan batu da ake tattaunawa a kansa, kusan kashi 90 suna dora laifin ne a kan Shugaba Buhari da zargin sa da gazawa a fannin tsaro.
Juya baya - Sharhi daga Halima Umar Saleh
Idan aka ce akwai ranar da al'ummar arewacin Najeriya da dama za su juya wa Shugaba Buhari baya ko su ga laifinsa kan wani abu, lallai za a iya musu a kan haka.
Tun a shekarar 2002 da Buhari ya fara nuna sha'awar yin takara a Najeriya, miliyoyin al'ummar kasar ke nuna masa kauna da shaukin son ganin ya cika wannan buri nasa. Ya shafe tsawon shekara 13 yana wanan fafutuka kafin ya samu darewa mulkin kasar a 2015.
Kuma a dukkan lokutan yakin neman zabensa an sha jin sa yana yin tur da salon mulkin gwamnatin PDP da nuna gazawarta wajen shawo kan matsalar rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.
Hakan ce ta sa 'yan kasar da dama suka dinga murnar samun nasararsa a karon farko a 2015, da yakinin cewa mai share musu hawaye ya zo.
Sai dai duk da cewa an samu raguwar tashin bama-bamai a wasu manyan biranen Najeriya bayan hawan sa ba kamar lokacin Jonathan ba, sai dai hakan ba ya nufin ya kawo karshen rikicin Boko Haram din Kungiyar ta ci gaba da ayyukanta musamman a jihihi Borno da Yobe.
Sannan wani abu da ake gani sabo ne ya kuma fara bayan hawan Buhari mulki shi ne hare-haren 'yan bindiga a arewa maso yammacin kasar a jihohin Katsina da Zamfara da Sokoto da Kaduna da kuma Niger.
A cikin watan Mayun da ya gabata Kungiyar nan mai bincike kan tashe-tashen hankula a kasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe mutane fiye da dubu takwas a rikicin arewa maso yammacin kasar cikin shekaru 10.
A rahoton da ta fitar, Kungiyar ta ce kawo yanzu kokarin hukumomi ya gaza kawo karshen tashin hankalin, wanda ya fi shafar jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina da kuma Kaduna.
Baya ga wannan kuma an yi ta shan fama da matsalar satar mutane don kudin fansa a wasu garuruwan da kuma kan manyan titunan kasar. Sai dai za a iya cewa an samu saukin wannan lamari a watannin baya-bayan nan musamman bayan bullar annobar cutar korona.
Masu sharhi a kasar da dama sun sha cewa a yanzu mafi yawan masoyan Shugaba Buhari sun dawo daga rakiyarsa, kuma ga alama babu wata hobbasa da gwamnatin da hukumomin tsaro ke yi don kawo karshen lamarin, duk da cewa dai suna ikirarin hakan.
Sun kara da cewa ga alama 'yan Najeriya dai ba su yarda da wannan ikirari ba, a takaice ma dai a iya cewa ba sa ganin wani kokarin gwamnatin da ya wuce yin tur da harin a duk lokacin da ya faru.
A farkon makon nan an yi zanga-zanga a Katsina inda aka ga mutane suna ta ƙona allunan tallar jam'iyyar APC da na Shugaba Buhari da Gwamna Aminu Masari, abin da wasu ke gani a matsayin tura ce ta kai al'ummar jihar bango, wacce kuma ita ce jihar da shugaban ya fito.
Barista Bulama Bukarti wani lauya ne kuma mai sharhi kan al'amuran tsaro a kasar, a wata hira da BBC ya ce: "Na sha fada cewa mutane za su dauki doka a hannunsu idan gwamnati ba ta yi abin da ya dace kan lamarin tsaro ba, mutane za su ci gaba da yin zanga-zangar nuna adawa da mulkin nan.
"Wannan abu ne ya sa jami'yyar PDP ta fadi a zaben 2015, saboda yadda aka shafe shekaru ba tare da ta magance rikicin Boko Haram ba.,'' in ji shi.
A makonnin baya da aka yi hare-hare Shugaba Buharin ya sha alwashin kawo karshen lamarin bayan inda ya ce za a tura sojoji yankunan. Yanzu abin a jira a gani shi ne ko wane mataki shugaban zai dauka nan kusa.
0 Comments: