A ranar Talata ne ake sa ran kwamitin da ke tantance masu neman tsayawa takarar shugaban ƙasar Najeriya ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Jam'iyyar APC, John Oyegun, zai ci gaba da tantance sauran masu neman tsayawa takara.
Ranar Litinin ne kwamitin ya soma tantance masu neman takarar.
Ana tantance masu neman takarar ne gabannin gudanar da zaɓen fitar da gwanin da za a gudanar na jam'iyyar tsakanin shida zuwa takwas ga watan Yunin 2022.
Ana gudanar da aikin tantancewar ne a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja babban birnin Najeriya.
Cikin waɗanda aka tantance a karon farko akwai tsohon gwamnan Jihar Legas Bola Tinubu da Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru da tsohon Ministan Sufuri Chibuike Amaechi da tsohon Gwamnan Ogun Ibikunle Amosun.
Sauran sun haɗa da tsohon ƙaramin Ministan Ilimi Chukwuemeka Nwajiuba da Gwamnan Ebonyi Dave Umahi da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ken Nnamani da tsohon Gwamnan Zamfara Sani Yarima.
Akwai kuma Felix Nicholas da Sanata Borroffice da Mrs Uju Ken-Ohaneye da Fasto Tunde Bakare
Sauran masu neman takarar da za a tantance a ranar Talata 31 ga watan Mayu kuwa sun haɗa da:
Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo na daya daga cikin na farko-farko da suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.Osinbajo, wanda daga Kwamishinan Shari'a na Jihar Legas ya zama mataimakin shugaban ƙasa na ɗaya daga cikin waɗanda ake sa ran za a tantance a ranar Talata.
Asalin hoton, Twitter
Gwamnan Jihar Ekiti kuma shugaban gwamnonin Najeriya Kayode Fayemi na daga cikin waɗanda ake sa ran za a tantance su a ranar Talata.
Gwamna Fayemi ya kasance ministan albarkatun ƙasa a lokacin mulkin Shugaba Buhari daga 2015 zuwa 2018 kafin ya tsaya takarar gwamna karo na biyu wanda dama ya taba yin gwamnan Jihar Ekiti daga 2010 zuwa 2014.
Asalin hoton, Twitter/@sen_ahmedlawal
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmed Lawan na daga cikin waɗanda za a tantance domin tsayawa takar shugaban ƙasa ƙarƙashin Jam'iyyar APC a ranar Talata.
Sanata Lawan wanda asalin ɗan Jihar Yobe ne, ya soma wakilci tun daga 1999 a matsayin ɗan Majalisar Wakilai, inda a 2007 ya koma Majalisar Dattawa kuma har yanzu yana a majalisa.
Yahaya Bello
Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello na daga cikin waɗanda ke neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin Jam'iyyar APC.
Yahaya Bello kusan shi ne ke da mafi karancin shekaru cikin mutanen da suka fito karkashin inuwar jam'iyyar APC suna neman mulkin Najeriya. Gwamnan yana da shekaru 46 a duniya.
Rochas Okorocha
Tsohon Gwamnan Imo kuma ɗan Majalisar Dattawa, Sanata Rochas Okorocha, mai shekara 59, na daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa a APC.
Sai dai ana ƙila wa ƙala kan ko zai iya halartar tantancewar sakamakon yana tsare a hannun hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC bayan kamun da ta yi masa kwanakin baya.
Dimeji Bankole
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Honarabul Oladimeji Bankole na daga cikin waɗanda ake sa ran tantancewa a ranar Talata.
Bankole shi ne Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya na tara kuma shi ne kakakin majalisar mafi ƙarancin shekaru a tarihin Najeriya inda ya zama kakakin yana da shekara 37.
Sauran waɗanda ake sa ran tantancewa a ranar Talata
Gwamnan Cross River, Farfesa Ben Ayade
Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu
Tsohon Ministan Watsa Labarai, Chief Ikeobasi Mokelu
Tsohon Ministan Harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio
Akwai kuma Mista Tein Jack-Rich

Gaskiya ya kamata ku cigaba da sabunta mana wannan shaf na madubiya.
ReplyDeleteDomin mu rinka zuwa muna karanta sabbin labarai.
Shafin: hausaedown.com.ng.