Me ya sa marigayi Abba Kyari ya yi kaurin suna a Nigeria?
A ranar Juma'a 17 ga watan Afirilun 2020 Allah Ya yi wa shugaban ma'aikata a fadar shugaban Najeriya Malam Abba Kyari rasuwa bayan ya yi fama da cutar Korona wadda ta zama annoba a fadin duniya.
Malam Abba Kyari, ya rasu a Legas inda ya tafi jinya bayan kamuwa da cutar ta Korona, yana da shekaru 67 a duniya kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ta nuna.
Shi ne babban jami'in gwamnati na farko da cutar Korona ta yi sanadin mutuwarsa a Najeriya.
Bayan kimanin makwanni uku yana jinya ya mutu, kana aka dauko gawarsa zuwa Abuja babban birnin kasar inda aka yi masa sutura.
A lokacin rayuwarsa, ana kallon Malam Abba, haifaffen jihar Borno, a matsayin mutum mafi karfin fada-a-ji a gwamnatin Muhammadu Buhari.
Hasali ma wasu na ganin ya kasance jagoran gwamnatin a kaikaice, saboda yadda suka yi imanin shi ne ke juya akalarta yadda yake so.
Ko shakka babu rawar da ya taka ta janyo masa suka, da bakin jini, yayin da wasu ke yabonsa da sambarka. Mutum ne da ya janyo ce-ce-ku-ce.
Mutuwarsa ta ja hankulan jama'a matuka a ciki da wajen Najeriya saboda imanin da mutane da dama suka yi cewa rawar da yake takawa a gwamnatin, lokacin da yake raye, na shafar rayuwar miliyoyin jama'ar Najeriya.
Karfin ikon Abba Kyari

Masu lura da lamura da dama na ganin idan akwai wani mutum guda da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shi, kuma yake takama da shi a gwamnatinsa, to shi ne marigayi shugaban ma'aikatan fadarsa Malam Abba Kyari.
Masu sharhi na cewa ya fi kowane jami'in gwamnati yawan ganawa da shugaba Buhari.
Watakila wannan asali ya samu, domin shugaba Buhari ya bayyana cewa tun shekaru 42 da suka gabata, wato lokacin marigayin na matashi dan shekara 20 da 'yan-kai, suka hadu kuma suka saba, har zuwa lokacin da mutuwa ta raba su.
Shugaban kasar, a sakonsa na ta'aziyya, ya ce ya yi rashin ''amini kuma mai kishin kasa'' wanda ya yi aiki tukuru a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.
To sai dai masu sharhi da ma wasu talakawan Najeriya na ganin Malam Abba Kyari ya samu iko da karfin fada-a-ji fiye da kima a gwamnatin Muhammadu Buhari inda wasu suka yi zargin cewa shi ke juya akalar gwamnatin a lokacin yana raye.
Wasu na ganin hatta ministoci da sauran masu rike da mukamai, tsohon shugaban ma'aikatan ne ya amince da nadin galibinsu, kuma duk wanda ba ya dasawa da shi, to zai yi wahala ya yi wani tasiri ko samun karbuwa a gwamnatin.
Wannan lamari ya sanya mutane da dama sun kalli Malam Abba a matsayin kadangaren bakin tulu..
Ba mutane na nesa ne kawai suka yi korafi ba. Hatta mai dakin shugaban kasa Aisha Buhari ta yi korafin cewa wasu mutane 'yan kalilan sun kankane gwamnatin mai gidan nata, suna kuma hana ruwa gudu.
Ko da yake ba ta ambaci sunan wani mutum a bainar jama'a ba, to amma masu lura da lamura da dama na ganin ta bi sahun wasu 'yan Najeriya ne masu korafi kan wasu makusanta shugaban kasar irin su marigayi Abba Kyari.
Wasu na ganin ta yi korafin ne saboda ita ma an hana ta sakat.
Haka nan, a kwanakin baya wasu kafofin watsa labarai a Najeriya sun ambato babban mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaron kasa, Babagana Monguno, na nuna rashin jin dadinsa kan salon Abba Kyari, yana cewa marigayin na yi masa katsalandan cikin aikinsa da ya shafi tsaron kasa.

Bayan sake rantsar da shugaba Muhammadu Buhari domin wa'adin mulki na biyu a watan Mayun 2019, shugaban kasar ya tayar da kura lokacin da ya bayyana karara cewa duk wanda ke son ganawa da shi - ko da ministan gwamnatinsa ne ko gwamna - bare kuma bako ko kuma mai ziyara - to dole ya bi ta wajen Abba Kyari.
Shugaba Buhari ya ba da umarnin ne a watan Agustan 2019 yayin rantsar da ministocinsa domin wa'adin mulki na biyu. Wannan lamari ya janyo manyan batutuwa akalla guda biyu.
Wasu na ganin shugaba Buhari ya kara lafta wa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar iko a daidai lokacin da 'yan kasar da dama ke ganin shi ne ma yake hana ruwa gudu a gwamnatin.
Wasu kuma na ganin umarnin shugaban kasar ya kaskantar da ministocinsa duk da cewa bisa tsarin mulki sun fi shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa karfin iko ko girman mukami.
To amma jami'an gwamnatin Buhari sun kare matakin da cewa ai da ma Malam Abba Kyari shi ne Sarkin Fada, don haka duk mai son ganin shugbaba sai ya bi ta hannunsa.
Kuma aikinsa a cewarsu shi ne kare muradin shugaba Buhari da kuma tsara jadawalin aiki a fadar shugaban kasar domin kauce wa rudani da tafiyar da lamura rambatsau. Don haka aikin na cikin hurminsa.
Wani mai sharhi kan lamuran siyasa, Dr Abubakar Kari, ya ce wani abu da ya jawo wa Abba Kyari bakin jini kuma ya sa aka kasa fahimtarsa shi ne irin karfin iko da aka ba shi wanda ''ba sabon ba ne a Najeriya''.
Dr Kari ya ce ba a taba yin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da aka bai wa karfin iko kamar marigayin ba.
0 Comments: