Kano ta maida wani mutum da ya kamu da coronavirus Jigawa – NCDC
Masu fama da cutar korona a Kano yanzu sun koma 36 bayan gwamnatin jihar ta mayar da wani dan asalin jihar Jigawa da ya kamu da cutar, zuwa mahaifarsa a karshen mako.
A cikin mako daya kacal adadin masu cutar korona a Kano ya kai 37 kafin mayar da mutumin zuwa Jigawa, yayin da jita kuma Jigawa a yanzu take da mutum biyu masu cutar.
Sai dai kwamishinan lafiya na Jigawa Abba Zakari ya shaida wa BBC cewa a lissafinsu, mutum daya ne mai cutar a jihar - wanda aka samu a Kazaure.
Saboda a cewarsa "shi da ya taho daga Kano ai na Kano ne, kawai dai sun ce ba za su ajiye shi a wurinsu ba, saboda dan Jigawa ne muka taho da shi,"
Ya kara da cewa an yi wa mutumin gwaji ne a Kano kuma "ba su kai shi cibiyarsu ba saboda mutumin Jigawa ne,"
"Aka kawo shi cibiyar killace masu cutar a Jigawa, sa'ar da muka yi daman daga Legas ya taho bai ma samu ya shiga jihar Jigawa ba saboda haka ba shi da mutanen da ya yi mu'amala da su,
"Sai wani yaro guda daya wanda suke tare suna cin abinci tare, shi mun masa gwaji mun ga cewa ba shi da wannan cuta amma duk da haka mun killace shi zuwa nan da kusan kwana bakwai zuwa takwas,"
"Idan bai nuna alamar wannan cuta ba za mu sake yi masa gwaji dai kuma sai mu sake shi," kamar yadda kwamishinan ya bayyana.
Tun da farko gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da bullar cutar covid-19 a karon farko a jihar cikin karamar hukumar Kazaure ranar Lahadi.
Mutumin dan asalin Jigawa ne da ya koma jihar daga Enugu kuma gwaji ya tabbatar yana dauke da cutar bayan ya nuna alamunta.
Kwamishinan ya bayyana cewa tuni suka fara gudanar da binciken mutanen da suka yi mu'amala da matafiyin domin a killace su tare da yi musu gwajin cutar.
Ya ce bullar cutar a yankin Kazaure ya sa gwamnati daukar matakin kulle garin na tsawon mako daya domin hana bazuwar cutar zuwa wasu sassan jihar.
"Wannan mataki zai fara ranar Litinin karfe 12 na dare, mun riga mun gano mutanen da suka yi hulda da shi,"
"Akwai wadansu mutane na kusa da shi mutum uku, akwai wasu mutane bakwai daga waje," in ji kwamishinan.
A yanzu dai ana da masu cutar korona a Najeriya 627 bayan da NCDC ta sanar da karin mutum 86 da suka kamu da cutar - adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar cikin kwana daya a kasar.
0 Comments: