Sunday, July 5, 2020

Lewandowski ya ci kwallo fiye da 50 a kakar bana

Lewandowski ya ci kwallo fiye da 50 a kakar bana



Robert Lewandowski ya zura kwallo 51 a raga a wasa 44 da ya yi wa Bayern Munich a kakar bana

Robert Lewandowski ya ci kwallo sama da 50 a kakar bana, bayan da Bayern Munich ta doke Bayer Leverkusen 3-2 ta lashe kofin Jamus na 20 jumulla.

Bayern Munich ce ta fara cin kwallo a bugun tazara ta hannun David Alaba sai Serge Gnabry ya kara na biyu sannan Lewandowski ya ci na uku a fafatawar.

Leverkusen ta farke daya ta hannun Sven Bender, sai Lewandowski ya ci na hudu na kuma biyu a wasan, yayin da Leverkusen ta kara zare daya a bugun fenariti ta hannun Kai Havertz.

Bayern Munich ta kafa tarihin buga wasa 26 ba tare da an doke ta ba a jere, kuma canjaras daya ta buga tun daga cikin watan Disambar 2019.

Haka kuma kungiyar ta kafa tarihin cin wasa 17 a jere.

Kwallo biyun da Lewandowski ya zura a ragar Leverkusen ya sa ya ci 51 a karawa 44 da ya yi wa Bayern Munich a bana.

Bayern Munich ita ce ta lashe kofin Bundesloiga na bana ga kuma na kalubalen Jamus da ta dauka ranar Asabar kuma karo na 13 tana cin kofi biyu a jere a kakar tamualar Jamus.

Bayern Munich, wacce ke fatan lashe kofi uku a bana za ta kara da Chelsea a gasar Champions League ta kungiyoyi 16 da suka rage a wasannin.

Bayern ce ta doke Chelsea 3-0 a wasan farko da ta ziyarci Stamford Bridge.

Previous Post
Next Post

1 comment:

  1. How to place NHL picks & NHL predictions - legalbet.co.kr 우리카지노 계열사 우리카지노 계열사 betway betway betway login betway login 78Bongo Casino: 100% Bonus, 100% Welcome Bonus - Casino

    ReplyDelete