Ɗaliban Kankara: Har yanzu ba a ji ɗuriyar 'ɗalibai 333' ba
Har yanzu ba a ji ɗuriyar ɗaliban makarantar sakandaren Kankara ta jihar Katsinan Najeriya da ƴan bindiga suka yi awon gaba da su ranar Juma'a ba.
Hakan na faruwa ne duk da zaratan sojoji da 'yan sanda da gwamnatin Najeriya ta aika domin gano ɗaliban.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya ce an aika zaratan sojojin ƙasa da na sama domin nemo ɗaliban baya ga jami'an 'yan sanda na musamman da Babban Sifeton 'yan sandan ƙasar Mohammed Adamu ya bayar da uarnin aikawa.
Hasalima Babban hafsan sojan ƙasa na Najeriya Janar Tukur Buratai ya isa garin Kankara ranar Lahadi.
Bayanai sun ce Janar Buratai ya gana da rundunar soji da ta ƙaddamar da binciken gano ɗaliban.
Babban Hafsan sojan na Najeriya ya tafi Kankara ne tare da tawagar gwamnatin Tarayya da ta ƙunshi ministan tsaro Janar Salihi Magashi mai ritaya da kuma mai ba shugaban ƙasa shawara kan sha'anin tsaro.
Bayanai masu cin karo da juna
Gwamnatin Katsina ta tabbatar da cewa ɗalibai 333 ne suka ɓata bayan harin da ƴan bindiga suka kai makarantar sakandaren ta Kankara.
Wata majiyar gwamnatin Katsina ta shaida wa BBC cewa Gwamna Masari ya tabbatar da hakan ne ga tawagar gwamnatin Tarayya ƙarkashin jagorancin bai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha'anin tsaro Babagana Monguno.
Gwamnan ya ce ana ci gaba da bincike a daji domin gano ɗaliban da ake tunanin ƴan bindiga sun sace.
Sai dai Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa yara da dama sun gudo yana mai cewa yara 10 ne kawai suka rage hannun ƴan bindigar.
A cewarsa, yaran da suka tsere daga hannun maharan sun ce yara 10 ne ke hannun ɓarayin ƙasa da yawan ɗaliban da malaman makarantar suka bayyana.
"Wasu daga cikin yaran da suka gudu daga daji sun ce yara 10 ne ƴan bindigar suke garkuwa da su," in ji shi.
Sai dai ya ce sai an bincika sannan domin sun warwatsu a daji saboda ɗimauta daga ƙarar harbe-harben bindiga.
Kakakin na shugaban Najeriya ya ƙara da cewa jami'an tsaro sun yi wa yankin da suke tunanin ƴan bindiga na garkuwa da ɗaliban da suka sace a Kankara ƙawanya.
Ya kuma ce kusan ɗalibai 200 suka dawo gida kuma wasu daga cikin iyayen yaran sun karɓi ƴaƴansu da suka fito daga daji yayin da kuma ake ƙoƙarin tantance yawansu da waɗanda suka dawo.
Mata sun yi zanga-zanga
Wasu hotuna da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna wata mace na jagorantar zanga-zanga a garin Katsina domin matsa wa gwamnati lamba kan ceto yaran nasu.
Matan riƙe da kwalaye sun buƙaci gwamnatin Najeriya ta yi gaggawar ceto ɗaliban suna masu yin tur da sace su.
A daren Juma'a ne ƴan bindiga suka afka makarantar sakandaren ta maza zalla da ke garin Ƙanƙara suka sace ɗaliban.
Wasu bayanai sun ce akwai ɗalibai fiye da 600 a yayin da aka kai harin, sai dai kakakin rundunar 'yan sandan Katsina, DSP Gambo Isa, ya shaida wa BBC cewa tuni aka gano ɗalibai fiye da 200.
Iyayen ɗaliban makarantar na jiran tsammani game da labarin ƴaƴansu, inda suka je makarantar domin sanin halin da 'ya'yansu ke ciki.
Me hukumomi suka ce da farko?
Sanarwar da Malam Garba Shehu ya fitar ranar Asabar ta ce an gano maɓoyar maharan har ma sun yi artabu da jami'an tsaro.
Rundunar ƴan sanda ta ce an kashe ɗaya daga cikin maharan kuma jami'inta ɗaya ya ji rauni, yayin da ta ce sufeton janar na ƴan sandan Najeriya ya tura ƙarin jami'ai domin kuɓutar da ɗaliban.
Ƴan Najeriya da iyayen ɗaliban na dakon sanarwa daga gwamnatin tarayya ko ta jihar Katsina game da inda aka kwana kan batun kuɓutar da ɗaliban na makarantar Kankara.
Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da sace ɗaliban amma gwamnatinsa na fuskantar matsin lamba, musamman kan yadda lamarin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a arewacin Najeriya.
Sace ɗaliban na zuwa bayan a ƙarshen watan da ta ya gabata, ƴan Boko Haram suka yi wa manoma yankan rago a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashi.
Iyayen yaran da aka sace sun bayyana wa BBC irin mawuyacin halin da suka shiga tun da aka sace 'ya'yansu.
Mahaifin wasu ɗalibai biyu ya shaida mana cewa tun da lamarin ya faru suke cikin damuwa "domin duk lokacin da aka ce yaronka ya ɓata dole ka shiga damuwa, don gara ma a ce mutuwa ya yi."
Ya ce mahaifiyar yaran ta shiga damuwa sosai ko da yake sun fawwala komai ga Allah.
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, wanda ya ziyarci makarantar ranar Asabar, ya bayar da umarnin rufe ɗaukacin makarantun sakandare na kwana da ke faɗin jihar.
0 Comments: