Thursday, December 17, 2020

ZABEN 2023: Jonathan Na Da Damar Tsayawa Takarar Shugabancin Nijeriya A Zabe Na Gaba, Cewar Jam'iyyar PDP

ZABEN 2023: Jonathan Na Da Damar Tsayawa Takarar Shugabancin Nijeriya A Zabe Na Gaba, Cewar Jam'iyyar PDP

Daga Comr Abba Sani Pantami

Jam'iyyar PDP da ta mulki Najeriya na tsawon shekaru 16 ta ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na da hurumin tsayawa takarar zaben shekarar 2023 idan yana bukata.

Shugaban Jam’iyyar Uche Secondus ya sanar da haka, inda yace cewa ya zuwa yanzu Jam’iyyar ba ta yanke hukunci dangane da karba karba ko inda ake sa ran ‘dan takaran zaben shekarer 2023 zai fito ba.

Secondus ya ce Jam’iyyar na jiran rahotan kwamitin da ke nazari kan abın da ya faru lokacin zaben shekarar 2019 daga hannun kwamitin da Gwamnan Bauchi Bala Muhammed ke jagoranci, domin gano abin da ya sa Jam’iyyar ta sha kaye.

Bayan kwashe shekaru 6 a karagar mulki, Jonathan ya fadi zaben shekarar 2015, lokacin da Jam’iyyar APC ta gabatar da Muhammadu Buhari a matsayin ‘dan takara, yayın da tsohon shugaba Jonathan yaki tsayawa zaben shekarar 2019.

Shugaban PDP ya gargadi Jam’iyyar APC mai mulki da ta daina kusantar ‘yayan ta ganin yadda ta dauke Gwamnan Ebonyi, David Umahi, yayin da kuma take zawarcin shugaba Goodluck Jonathan.


Previous Post
Next Post

0 Comments: