Tsaro a kasarmu da namu laifi
Sau nawa muka aje ra'ayi, muka dukufa ga yiwa shugabaninmu da kasarmu addu'ar neman mafita da samun sauki akan wadanan masifun dake kara azzara da sanya al'umma cikin wahala da rashin kwanciyar hankali?
Sau nawa muka tausayawa masu rauni daga cikinmu ba tare da neman asani ba, ko muka sada zumunta ko muka ziyarci yan uwa ko makwabta dake fama da wahala don taimaka musu ko yin jaje ko tausayawa akan jarrabawar da aka aza musu?
Ko kayi gyara ayau, ko ka ci gaba da hangen laifin wasu kana take naka; don ganin kai ka hau wani tudun tsira, har da hura hanci abin kuma yana ta'azzara.
Wannan ba shine mafita ba, mafita itace, mu tuba, mu zauna mu yiwa kanmu karatun ta natsu don samun sauki da taimakon Ubangiji Allah (SWT).
Hakika wannan masifar ta wuce dora laifi akan shugabani su kadai, ko neman siyasantar da ita; ko ganin cewar, kai ka tsira, ba ruwanka da halin da wasu suke ciki. Tabbata kowa yana da rawar da zai taka ga samun nasara da ganin an shawo kan matsaloli da barazana da ake ciki akan tsaro, musifu da ake ta haduwa dasu a cikin al'umma.
Mu dukufa ga yiwa shugabani addu'a tagari da basu uzuri akan barazana da kalubalen da suke fuskanta ga gudanar da ayyukansu na lamuran mulki a yau; tare da sanya kasarmu da jihohinmu a cikin addu'oi ga neman sauki da maganin wannan lamarin baki daya.
Sha'anin tsaro fa ya wuce aikin gwamnati ko jami'an tsaro su kadai; kowanenmu mu sani, yana da hakki da dama mai yawa don bada gudumuwarsa ya taimakawa da shawara, addu'a don samun nasara akan yaki da wadanan masifun a gida, unguwa, gari, karamar hukuma, da jaha ko kasa baki daya.
Mu yiwa juna uzuri da fatan alheri da taimakawa ga bayar da rahoto ko bayanai akan dukkan wani ko wasu dake da barazana ga zaman lafiya al'umma.
Mu daina jiran sai ta faru, muce ai daman, mun san haka zata kasance. My sani dukkanmu makiyaya ne, ba shakka sai Allah Ya tambaye mu daya bayan daya akan abin da aka bamu kiwo da yadda muka aiwatar dashi.
Allah Yayi ma al'ummarmu mafita ya tallafawa shugabaninmu dake akan gaskiya ga wannan aikin na yaki da ta'addanci da sauran masifu dake addabar jama'a. Amin.
- Yusuf Dingyadi, Sokoto